Firaministan Libiya Abdulhamid Dibeybe na ziyara a Ankara Babban Birnin Turkiyya.
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne ya gaiyaci Dibeybe.
Shugaba Erdogan ya tarbi Dibeybe a fadar gwamnati da buki na musamman.
A karkashin ziyarar, za a tattauna kan batutuwan makamashi da lafiya, sannan za a duba batun komawar 'yan kasuwar Turkiyya Libiya wadanda rikici ya sanya su suka dakatar da aiyukansu.
News Source: ()