Filin jirgin saman Istanbul ya karbi bakuncin fasinjoji sama da dubu 100 a ranakun 25- 26 -27 na watan Yunin.
Hakan na nuni ga mafi yawan fasinjojin da filin jirgin ya samu tun bayan bulluwar kwayar cutar (Kovid-19).
A cikin bayanin da aka yi akan shafukan sada zumunta na Hukumar Kula da Filin Jirgin saman IGA (Babban Filin Jirgin saman Istanbul), an bayyana cewa,
"Mun fuskanci lokutan da suka fi kowane lokaci a lokacin annobar ta hanyar karbar bakuncin fasinjoji sama da dubu 100 a kullum a ranakun 25 zuwa 26 na Yuni. Godiya ga matakan kula da tsafta da muka dauka, a shirye muke mu yi maraba da dukkan bakin da ke shirin tafiya a cikin hanya mafi kyau."