Filin jirgin saman Istanbul da kanfanin jiragen saman kasar sun sake kafa tarihi

Filin jirgin saman Istanbul da kanfanin jiragen saman kasar sun sake kafa tarihi

Sabon filin tashi da saukar jirgen saman Istanbul da kanfanin Jiragen Saman Turkiyya sun kara yawan safarar da suke yi a ko wace rana.

A cewar bayanan da aka samu, fasinjoji dubu 37 da 90 ne suka yi amfani da filin jirgin saman Istanbul a jiragen cikin gida yayin da fasinjoji dubu 79 da 90 a matakin kasa da kasa a rana daya.

Filin jirgin sama, wanda jimillar fasinjoji dubu 116 da 180 suka yi amfani da shi, ya sami É—ayan ranar da aka fin safara duk da yayin sabon nau'in cutar coronavirus (Kovid-19).

Kanfanin jirgin saman Turkiyya THY, wanda shine kamfanin jirgin sama mafi yawan jirage a sararin samaniyar Turai a cikin watanni 5 na 2021, a ranar 25 ga watan Yuni ya sami nasarar  saukar jiragen sama har dubun 1,065 a rana wanda bai taba samu ba tun bayan bulluwear kwayar cutar Korona.


News Source:   ()