A tsakanin watan Janairu da Afrilun 2021, fasinjoji miliyan 5 da dubu 549 da 68 ne suka tashi da sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Sabiha Gokcen dake birnin Istanbul din Turkiyya.
Sanarwar da aka fitar daga ofishin kula da filin tashi da saukar jiragen sama na Sabiha Gokcen ta ce, a watanni 4 na farkon wannan shekarar jirage dubu 41 da 785 ne suka tashi da sauka a bangaren safarar cikin gida da na kasashen waje.
A bangaren safarar jiragen kasashen waje an yi hidima ga fasinjoji mliyan 1.6.
A watan Afrilu kuma jimillar fasinjoji 1.3 ne suka tashi da sauka a filin jirgin na Sabiha Gokcen.
News Source: ()