An bayyana cewar, farin dango sun yi mummunar barna a gonakin kasar Tanzaniya da ke gabar tekun Indiya a gabashin Afirka.
Jami'in yankin Kilimanjaro da ke arewacin Tanzaniya, Onesmo Biswelu ya shaida cewa, farin dangon sun shiga Tanzaniya daga Kenya tare da mamayar arewacin kasar.
Biswelu ya fadi cewa, farin dangon sun lalata amfanin gona da yawa, an aike da jiragen sama na musamman da ma'aikatan gona don yin feshin magani tare da korar farin.
Ya ce, "Mun samu nasarar rage farin da kuma takaita barnar da suke yi."
Tsawon shekaru kasashen gabashin Afirka da suka hada da Kenya, Itopiya da Sudan su ke fama da farin dango.
Ofishin Abinci da Noma na Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ya sanar da cewa, ana bukatar dala miliyan 38 don yakar mamayar da farin dango ke wa yankunan.
Farin dangon na janyo matsalar samar da abinci inda a shekarar da ta gabata suka lalata dubunnan daruruwan hektoci na amfanin gona.
Farin dangon sun kai miliyan 40 zuwa 80 kuma a kowacce rana suna iya cinye abincin da mutane dubu 35 za su iya ci.
Kuma a kowacce rana suna iya yin tafiyar kilomita 150.