Fari: Mutane miliyan 2,1 na bukatar taimakon abincia Itopiya

Fari: Mutane miliyan 2,1 na bukatar taimakon abincia Itopiya

Sakamakon matsalar karancin ruwan sama, mutane miliyan 2,1 na bukatar taimakon abinci a jihar Somaliya da ke Itopiya.

Ofishin Aiyukan Jin Kai na Majalisar Dinkin Duniya ya shaida cewa, akwai yankuna 74 a Somaliya da ke fama da matsalar abinci saboda farin da aka fuskanta.

Yankunan Dawa, Liban, Afdher, Shabelle, Siti da Jarar ne suka fi fuskantar matsalar farin, mabubbugan ruwa da ke yankunan sun bushe. Ana yin dogon layi don samun ruwan amfani a yankunan.

Ana bukar kusan dala miliyan 65 don kaiwa jama'ar yankunan ruwan sha da motocin tanka.


News Source:   ()