Ministan Baitulmali da Kudi na Turkiyya Lutfi Elvan ya gana da Ministar Kudi da Hidima ta Malta Clyde Caruana a Ankara Babban Birnin Turkiyya.
Elvan ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewa, ya gana da takwararsa ta Malta a Ma'aikatarsa.
Ya ce, "Mun gana da Ministar Kudi da Hidima ta Malta Clyde Caruana. A ganawar da muka yi a Ma'aikatarmu mun tattauna kan hadin kai tsakanin kasashenmu."
News Source: ()