A Najeriya an haramta ta'ammuli da sarrafa kudaden "crypto currency" ko kuma "bitcoin".
Babban Bankin Najeriya ya shaida cewa, sakamakon yadda ake amfani da irin wadannan kudade na "crypto currency" ko kuma "bitcoin" wajen taimakawa ta'addanci da satar kudade ne ya sanya aka haramta ta'ammuli da su a kasar.
An bayyana cewar, irin wadannan kudade sun sabawa dokokin Najeriya, sakamakon haka Babban Bankin Kasa (CBN) ya umarci bankuna da su rufe dukkan asusunan da suke da irin wadannan kudade a cikinsu.
Najeriya ce kasa ta 2 a duniya da ta fi ta'ammali da "crypto currency" ko kuma "bitcoin".