A Denmark an fara karkashe kaji da agwagi sakamakon bullar murar tsuntsaye ta H5N8 da aka samu.
Sanarwar da hukumar Kula da Ingancin Kayan Abinci ta Denmarka ta fitar ta ce, an samu kaji da agwagin da ke wani gidan gona a kauyen Vinderup na gundumar Holstebro dauke da cutar murar tsuntsaye nau'in H5N8.
An bayyana fara kashe kaji dubu 10 da agwagi dubu 9 da ke gidan gonar.
Daga 2020 zuwa yau a karo na 15 kenan ana samun murar tsuntsaye a Denmark.
A watan Maris din shekarar da ta gabata an kashe talo-talo kusan dubu 65 inda a watanni 5 da suka gabata aka kashe tsuntsaye sama da dubu 100.