Bututun man fetur ya yi bindiga a Iran

Bututun man fetur ya yi bindiga a Iran

Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar bututun man fetur a jihar Huzistan da ke kudancin Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Iran ya shaida cewa, a yankin Fath Al-Mubin na garin Shush da ke jihar Huzistan ne ibtila'in ya afku a lokacin da bututun man fetur ya yi bindiga.

Bayanan farko da aka fitar sun bayyana cewa, sakamakon kwararar man, ma'aikata 3 sun rasa rayukansu.

Haka zalika an bayyana jikkatar wasu mutanen 4 sakamakon ibtila'in.

 


News Source:   ()