Biden: Sai Iran ta daina sarrafa Yuraniyom za mu janye mata takunkumai

Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya bayyana cewa, ba za su janyewa Iran takunkumai ba har sai ta dakatar da sarrafa makamashin Yuraniyom.

A karon farko bayan Biden ya hau mulki a ranar 20 ga Janairu ya tattauna da tashar CBS.

Da aka zo bangaren Iran a tattaunawar, Biden ya yi bayanai game da yarjejeniyar samar da makaman Nukiliya.

Da aka tambayi Biden kan cewar ko Amurka za ta janyewa Iran takunkumai kafin su fara zama tattaunawa sai ya ce,

"A'a. Sai sun fara dakatar da sarrafa Yuraniyom tukunna."

A baya gwamnatin Biden ta bayyana cewar za ta iya mayar da Amurka ga yarjejeniyar Nukiliya amma "bisa wasu sharudda".

Jagoran Iran Ayatullah Ali Hamaney ya ce, sai Amurka ta janye takunkuman da ta saka musu sannan za su cika dukkan sharuddan da ke cikin yarjejeniyar Nukiliya.

Ali Hamaney ya mayar da martani ta shafin Twitter ga Biden da ya sakawa Iran sharadin dakatar da sarrafa Yuraniyom inda ya ce,

"Mun fadi sharadinmu, ba komawa da baya".

A shekarar 2015 ne Iran tare da Amurka, China, Faransa, Jamus, Rasha da Ingila suka sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da sarrafa makamashin Yuraniyom da Iran din ke yi.

A ranar 8 ga watan Mayun 2018, tsohon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya cire kasarsa daga yarjejeniyar inda ya kakabawa Iran sabbin takunkumai.

A ranar 5 ga watan Janairun 2020 kuma gwamnatin Tehran ta sanar da ci gaba da sarrafa makamashin Yuraniyom sosai bayan dakatar da aiki da sharuddan da yarjejeniyar ta kunsa.


News Source:   ()