Beraye sun dagula al'amura a Ostireliya

A jihohin New South Whales da Queensland na kasar Ostireliya, beraye sun dagula al'amuran yau da kullum.

An bayyana cewa, samun mamakon ruwan sama ne ya janyo berayen suka farwa gidaje da gonakin jama'a.

Manoma sun bayyana cewa, berayen da aka kiyasta yawan su zai kai dubu dari biyar, sun lalata musu amfanin gona, wanda hakan ya sanya suka bukaci da a kawo musu taimako. Manoman sun nemi gwamnati da ta dauki matakin gaggawa.

A gefe guda kuma, an kai wasu mutane 3 asibitocin jihohin Tottenham, Walgett da Gulargambone bayan cizon su da berayen suka yi.

 


News Source:   ()