Bankin Duniya ya dakatar da baiwa Afganistan taimako

Bankin Duniya ya dakatar da baiwa Afganistan taimako

Bankin Duniya ya bayyana dakatar da baiwa Afganistan duk wani nau'i na taimako da tallafi.

Sanarwar da Kakakin Bankin Duniya ya fitar ta ce, suna da matukar damuwa kan halin da aka fada a Afganistan musamman ma game da cigaban mata a kasar.

Sanarwar ta ce, "Mun dakatar da biyan kudadenmu a Afganistan, muna kallon yanayin da ake ciki ta mahangar tsarinmu da manufofinmu tare da yin nazari."

Sanarwar ta kara da cewa, Bankin zai ci gaba da shawarta da tuntubar hukumomin kudi da cigaba na kasa da kasa, kuma an gudanar da bincike game da yadda za a kula da irin cigaban da aka samu a Afganistan da kuma wanzar da shi. Haka zalika za a ci gaba da taimakawa jama'ar kasar."


News Source:   ()