Bankin Duniya: Tattalin arzikin Turkiyya ya bunkasa a lokacin Korona

Bankin Duniya: Tattalin arzikin Turkiyya ya bunkasa a lokacin Korona

Tattalin arzikin Turkiyya ya bunkasa da kaso 1.8 cikin a shekarar 2020 yayin da kwayar cutar Korona ke cigaba da dakile lamurra, a cewar wata sanarwa da Daraktan Bankin Duniya na Turkiyya, Auguste Tano Kouame ya fitar.

Kouame ya jaddada cewa wannan bunkasa ne na tattalin arzikin kasar mai gwabi a yayin taron gabatarwa karo na 5 na Rahoton Kula da Tattalin Arzikin Turkiyya wanda Bankin Duniya.

Ya ce, rahoton ya hada da kimantawa game da tattalin arzikin Turkiyya da shawarwari don karfafawa da samun ci gaba a nan gaba.

"Kasashe da dama na kokawa da illar wannan annobar. Tattalin arzikin duniya ya ragu da kashi 4. cikin dari a bara, idan ka cire China, muna magana ne game da raguwa da kaso 5 cikin dari."

Annobar ta kara talauci a duk duniya. "Muna tunanin cewa a shekarar 2020, kusan mutane miliyan 100 a duniya sun fada cikin tsananin talauci"


News Source:   ()