Bankin Duniya: Mutane miliyan 7 sun fada bakin talauci a Najeriya

A Najeriya da kayan masarufi suka yi rashin gwauron zabi, mutane miliyan 7 ne suka fada cikin talauci  shekarar da ta gabata.

Bankin Duniya ya sanar da cewa, sakamakon yadda farashin kayayyakin masarufi ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya, a 2020 mutane miliyan 7 ne suka fada talauci a kasar.

A gefe guda, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, a shekaru 2 da suka gabata sun fitar da 'yan Najeriya miliyan 10,5 daga cikin talauci.

Buhari ya bayyana cewa, sun bawa manoma da masu kanana sana'a'i tallafi.


News Source:   ()