Kasar Ghana za ta karbi rancen dala miliyan 200 daga Bankin Duniya domin yaki da sabon nau'in kwayar cutar Coronavirus (Kovid-19).
A cewar rahoton da kwamitin kudi na Ghana ya wallafa, majalisar dokokin kasar ta Ghana ta amince da rancen dala miliyan 200 daga Babban Bankin Duniya domin yakin da kasar ke yi da Kovid-19.
Za a yi amfani da dala miliyan 137 daga cikin rancen dala miliyan 200 da za a samu daga Bankin Duniya don samar da allurar rigakafin Kovid-19, sauran kuma za a yi amfani da su ne don tallafawa kananan 'yan kasuwa da annobar ta shafa.
News Source: ()