Atisayen sojin Turkiyya mafi girma a teku

Atisayen sojin Turkiyya mafi girma a teku

Dakarun Ruwan Turkiyya na gudanar da atisaye mafi girma a tarihinta a tekun Aegean da Gabashin Bahar Rum.

Bayan atisayen Mavi Vatan da ake gudanar a watan Maris, a ranar Talatar nan an fara atisayen "Denizkurdu 2021" tare da jiragen ruwa 132, jiragen karkashin ruwa 10, jiragen sama 43, jirage masu saukar ungulu 28 da jiragen yaki marasa matuka 14.

Za a gwada yin hadin kai tsakanin rundunonin sojin sama da na kasa na Turkiyya, hukumomin gwamnati 10 da Turkish Red Crescent.

Akwai ma'aikta dubu 25,500 da ake gudanar da atisayen da su.

Atisayen Denizkurdu 2021, na dauke da dabarun yaki manya.

Daga ciki akwai mayakan waje, na ruwa, mayakan lantarki da mayakan kubutar da dakaru a karkashin teku.

A karshen atisayen, jiragen ruwa 83 za su ziyarci tashoshin jiragen ruwa 22 a tekunan Aegean da Gabashin Bahar Rum.

Sabanin yadda aka saba a shekarun baya, saboda annobar Corona ba za a budewa 'yan kasa jiragen su shiga ba.

Za a kammala atisayen Denizkrdu 2021 a Gabashin Bahar Rum a ranar 5 ga Yuni.


News Source:   ()