'Yan kasuwan Amurka sun yi kira ga Biden da ya farfado da kasuwanci da China

'Yan kasuwan Amurka sun yi kira ga Biden da ya farfado da kasuwanci da China

'Yan kasuwa a Amurka sun nemi gwamnatin shugaba Joe Biden da ta sake fara tattaunawar kasuwanci da China da kuma rage harajin shigo da kaya.

Dangane da labarin mujallar  The Wall Street Journal, wasu manyan kungiyoyin kasuwanci, da suka hada da Rukunin Kasuwancin Amurka, Kungiyar Masu Retaloli ta Kasa da Kungiyar Masana'antu ta Semiconductor, sun rubuta wasika ga Sakataren Baitulmali Janet Yellen da Wakilin Kasuwancin Amurka Katherine Tai kan batun.

A cikin wasikar, 'yan kasuwa sun bayyana cewa kasar China ta cika muhimman sharudda da alkawurra a yarjejeniyar ciniki.

A wasikar da aka tunatar akan bukatar mulkin Biden na mayar da fifiko ga jin dadin ma'aikata an bayyana cewa,

"Dole ne ajandar kasuwancin da ta shafi ma'aikaci ta kasance ta kula da  lissafin harajin Amurka da China. Ya kamaya a cire harajin dake cutar da manufa da muradun Amurka."
 


News Source:   ()