Sakamakon matsalar fari da karancin ruwan sama da ake fuskanta a kasar Madagaska dake tsibiri daya tilo a nahiyar Afirka, kasar ta fada matsalar karancin abinci.
Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka ta sanar da cewa, ana fuskantar babbar matsalar karancin abinci a Madagaska.
Wani mazaunin yankin dan kasar Mozambik Danis Huseyin ya bayyana cewa, wannan al'amari ya fi illata yara kanana wanda saboda karancin cimaka suke kamuwa da cututtuka da dama.
Huseyin ya kara da cewa, tsawon shekaru 3 ana fama da karancin ruwan sama a kudancin Madagaska, kuma ibtila'in yana janyo matsaloli a harkokin noma da kiwo.
Huseyin ya kuma ce, jama'ar yankin na gwagwarmayar rayuwa, akwai bukatar a kai taimakon gaggawa zuwa yankin.