Ana cigaba da kera sabbin motocin TOGG a kasar Turkiyya

Ana cigaba da kera sabbin motocin TOGG a kasar Turkiyya

Shekaru uku tun bayan kafuwarta a karkashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan a 2018, TOGG, Kanfanin  Mota ta Turkawa, na ci gaba da ayyukan samar da motocin ba tare da dakatawa ba.

An sanar da aikin mota na farko da Turkiyya ta kera a cikin gida a ranar 15 ga Mayu, 1961 mai suna "Devrim" (Juyin Juya Hali). Injiniyoyin Turkiyya sun ɗauki kwanaki 129 kawai don tsarawa, kerawa da gabatar da motoci guda 4 na Devrim waɗanda suke shirye don gabatarwa ga jama'a a ranar 29 ga Oktoba, 1961 yayin bikin ranar Jamhuriya a Ankara.

Koyaya, an dakatar da aikin bayan rashin isasshen mai ya sa wata mota ta makale a kan hanya lamarin da ya sanya ba 'a samu bayanai masu kyau ba.

Bayan haka "juyin juya halin mota na biyu" na kasar da Erdogan ya sake farfadowa dashi, an kafa kamfanin TOGG a hukumance a ranar 25 ga watan Yuni, 2018. An nada Mehmet Gurcan Karakas a matsayin babban jami'in gudanarwa a ranar 1 ga Satumba, 2018.

Erdogan ya gabatar da samfurin TOGG na lantarki C-SUV da C-Sedan a ranar 27 ga Disamba, 2019 ga jama'a a taron wanda ya sami halartar mutane sama da 2,000.


News Source:   ()