Tun daga farkon shekara zuwa yau an kai hare-hare sau 160 kan manyan turakun lantarki a fadin kasar Iraki.
Rahoton da aka fitar daga Ofishin 'Yan Sandan Kula da Makamashi da ke karkashin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ya bayyana cewa, daga farkon 2021 zuwa 10 ga watan Yuli an kai harin bam kan turakun lantarki 104 da hanyoyin sadarwar makamashin 54.
Rahoton da Ofishin 'Yan sandan Kula da Makamashin ya fitar ya ce, ana samu karuwar hare-haren bam kan cibiyoyin samarwa da rarraba lantarki a gabashin, arewaci da yammacin Iraki.
Sakamakon yadda wannan ta'asa ta ke janyo rashin samun isasshen lantarki, jama'ar kasar suke gudanar da zanga-zanga.
Mahukuntan Iraki sun dora alhakin kai hare-haren kan kungiyar ta'adda ta Daesh.