An zubar da allurar riga-kafin Corona miliyan 15 a Amurka

An zubar da allurar riga-kafin Corona miliyan 15 a Amurka

A kamfanin samar da magunguna na Johnson&Johnson da ke garin Baltimore na Amurka, an zubar da allurar riga-kafin Corona guda miliyan 15 sakamakon gaurayuwa da sinadaran hada magunguna.

Labaran da jaridar New York Times ta fitar na cewa, a kamfanin da ke Baltimore da ake samar da allurar riga-kafi na Johson&Johnson da AstraZeneca, an zubar da miliyoyin allurar riga-kafin Covid-19 na Johnson&Johnson.

Sakamakon lamarin an zubar da allurai miliyan 15, kuma Hukumar Kula da Ingancin Kayan Abinci da Magunguna ta Amurka ta fara gudanar da bincike.

Allurar Johnson&Johnson da ake karbar ta sau daya kawai, ana sa ran za ta hanzarta riga-kafin da ake yi a Amurka.


News Source:   ()