Sakamakon yawaitar zubar dusar kankara a Denver babban birnin jihar Colorado ta Amurka, an soke tashi da saukar jiragen sama fiye da dubu 2.
An soke tashi da saukar jiragen sama 750 ranar Asabar din da ta gabata, a ranar Lahadi kuma aka soke dubu 1300 sakamakon zubar dusar kankara a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke Denver.
Sashen Sufuri na Colorado ya sanar da cewa, dusar kankarar ta janyo an rufe hanyoyi da yawa, kuma an gargadi mutane da kar su yi tafiya idan ba ta kama dole ba.
News Source: ()