An samu nasarar motsa jirgin dakon kaya da ya tsaya a Mashigar Teku ta Suwaish

An samu nasarar motsa jirgin dakon kaya da ya tsaya a Mashigar Teku ta Suwaish

Sakataren Shugaban kasar Masar Ihab Memish ya bayyana cewa, an samu nasarar motsa jirgin ruwan dakon kaya da ya tsaya cak a Mashigar teku ta Suwaish.

Memish ya fitar da sanarwa a tashar talabijin ta kasa ta Masar cewa, an kubutar da jirgin dakon kayan kuma ya motsa a kan teku.

Kafafan yada labarai sun bayyana cewa, jirgin ruwan ya tashi tare da kama hanyar inda ya nufa tun farko.

A gefe guda, Shugaban Hukumar Kula da Mashigar Ruwa ta Suwaish usama Rabi ya shaida cewa, wasu karin manyan jiragen ruwa sun shiga aikin kubutar da jirgin ruwan 'Ever Given' da ya tsaya cak a Mashigar Teku ta Suwaish.

Rabi ya bayyana cewa, jiragen ruwa masu kugiya 12 ne suka yi aikin kubutar da jirgin 'Ever Given'.

A ranar 24 ga Maris ne jirgin ruwan dakon kaya ya tare hanyar wucewar jiragen ruwa a Mashigar Suwaish da ta ke daya daga cikin hanyoyin teku mafiya muhimmanci a duniya.

An samu cinkoson jiragen ruwa a mashigar sakamakon matsalar da jirgin 'Ever Given' ya janyo.


News Source:   ()