An sanar da cewa an samu bunkasar saŕrafa kayayyaki a kasar Turkiyya da karin kaso 1 cikin dari a watan Janairu da kuma karin kaso 11.4 cikin dari a shekara.
Hukumar Kiddiddigar kasar Turkiyya ce ta bayyana yanayin bunkasar harkokin kanfunan kasar ya zuwa watan Janairu.
Sassan fitar da ma'adanai da fasa duwatsu sun bunkasa da kaso 15.4 cikin dari inda aka kwatanta da na shekarar bara haka kuma sashen kaddarori ya samu karuwar kaso 12.1 cikin dari.
A watan Janairu sassan hakar ma'adanai da fasa duwatsu sun bunkasa da kaso kashi 6.8 cikin dari inda sashin kaddarori ya samu karuwar kaso kashi 1.1 cikin dari a watan.