An samu bunkasar fitar da sutura daga Turkiyya

An samu bunkasar fitar da sutura daga Turkiyya

A cikin watan Febrairu an fitar da tufafin fata na dala miliyan 129 da dubu 641 daga kasar Turkiyya zuwa kasashen waje. 

Hukumar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje ta bayyana cewa daga cikin kayyayaki na miliyan 85 da dala dubu 550 kaso 66 cikin darinsu suturan fata ne.

Kasar da tafi ko wace sayen kayyayakin da aka yi da fata ita ce kasar Rasha. 

A yayinda Rasha ta sayi kayayyakin fata daga Turkiyya na dala miliyan 9 da dubu dari 436 kasar Jamus ta sayi na miliyan 7 da dubu 361.

Haka kuma an samu karin fitar da kayayyakin fatan zuwa kasashen Afirka da karin kaso 14 , zuwa Asiya da karin kaso 10 cikin dari idan aka kwatanta da na bara. 

Haka kuma duk da matsalolin da Korona ta haifar an samu karin fitar da kayayyakin fatan zuwa kasashen Faransa da Holan. 

 

 


News Source:   ()