A karar da aka shigar da kuma binciken cin hanci da rashawa da ake yi a Saudiyya, an kama mutane 207 da suka hada da ma'aikatan gwamnati.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Saudiyya ta fitar da rubutacciyar sanarwa cewa, a tsakanin 11 ga Yuli da 9 ga Agusta an gudanar da bincike kan cin hanci, rashawa da amfani da ofishin gwamnati ta mummunar hanya.
Sanarwar ta bayyana an kama mutane 207 da suka hada da ma'aikata a ma'aikatun harkokin cikin gida, harkokin waje,shari'a, lafiya, ilimi da kasuwanci.
An fara shirin mika mutanen gaban kuliya.
A watan Maris din 2018 ne Sarkin Saudiyya Salman dan Abdulaziz ya amince da a kafa kwamitin musamman don yin nazari kan binciken cin hanci da rashawa da ake yi a kasar.