An gwada harba makami mai linzami kirar Turkiyya

An gwada harba makami mai linzami kirar Turkiyya

A lardin Sinop, an gwada harba makami mai linzami mai cin dogon zango da ake iya harba shi daga teku wanda kamfanin Roketsan na Turkiyya ya samar.

Sanarwar da fadar gwamnan Sinop ta fitar ta ce, makami mai linzamin da ake harba shi daga teku wanda kamfanin Roketsan ya samar, ya samu nasarar gwaji inda a yanzu za a fara samar da shi don sayarwa.

Kwamandan Rundunar Sojin Ruwan Turkiyya Admiral Adnan Ozbal da Gwamna Erol Karaomeroglu ne suka shaida yadda aka gwada harba makamin.

A bayanin da Ozbal ya yi ya ce "Kayanmu na kasa Atmaca tsaro ne ga aboki, kuma mai razanar da makiya ne."

 


News Source:   ()