‘Yan kasar Lebanon sun gudanar da zanga-zanga a Beirut babban birnin kasar don nuna adawa da tsadar rayuwa da matsalar tattalin arziki da faduwar darajar kudin kasar.
Masu zanga-zangar sun taru a sassa daban-daban na birnin, sun kona tayoyi, sun toshe wasu manyan tituna tare da rera taken yin Allah wadai da mummunan yanayin rayuwa da matsalar mai.
Jami'an tsaro, a gefe guda, sun kalubalanci masu zanga-zangar tare da bude babbar hanyar don zirga-zirgan ababen hawa.
Tattalin arzikin Labanon, wanda ta gurbace sabili da fuskar rarrabuwar kawunan siyasa dangane da addinai da mazhabobi daban-daban, na fuskantar babban rikici tun bayan yakin basasa na shekarar 1975-1990.
Canjin kudin cikin gida da kudaden kasashen waje na ci gaba da tabarbarewa musanmman a hannun 'yan kasuwa 'yan canji.