An fara wahalar man fetur a wasu sassan Najeriya

An fara wahalar man fetur a wasu sassan Najeriya

A Najeriya bayan da gwamnati ta sanar da ba za a kara farashin man fetur a watan Mayu ba, an fara wahalar man a wasu sassan kasar.

Wasu gidajen mai na rufe a kasar, a wasu gidajen mai da ke Abuja kuma ana samun dogayen layukan ababan hawa.
Ahmadu Bello da ke layin sayen man fetur ya bayyana cewa, ya yi jiran tsawon awanni 3 don sayen man fetur.
Bala ya ce, da yawa daga cikin gidajen man da ke Abuja Babban Birnin Najeriya na rufe.
Ya ce, "Gwamnati ba ta kara kudin mai ba amma rufe gidajen man na jefa mutane cikin wahala. Wadanda ba sa son jira a gidan mai na saya da tsada a cikin unguwanni a hannun 'Yan bumburutu."
Bala ya bukaci gwamnati da ta tsoma baki don ganin an bude gidajen man.
A shekarar da ta gabata sau 5 aka kara farashin man fetur a Najeriya.

News Source:   ()