An fara gwada riga-kafin Pfizer-BioNTech kan 'yan shekaru 6-11

An fara gwada riga-kafin Pfizer-BioNTech kan 'yan shekaru 6-11

Kamfanin Pfizer na Amurka da abokin aikinsa na BioNTech da ke Jamus sun sanar da fara gwada allurar riga-kafin cutar Corona (Covid19) kan masu shekaru 6 zuwa 11.

Sanarwar da aka fitar daga Pfizer ta bayyana cewa, an fara gwajin farko kan masu sadaukar da kawunansu, kuma ana hasashen a farkon shekara mai zuwa za a fara yin allurar ga yara kanana.

Sanarwar ta kuma ce, ana fatan samun sakamakon gwajin da aka yi kan yara masu shekaru 6 zuwa 11 a watanni 3 na farkon shekarar 2021, kuma a makonni masu zuwa za a samu sakamakon aiyukan samar da riga-kafi ga masu shekaru 11 zuwa 15.

 


News Source:   ()