An fara Babban Taron Hadin Kan Kasashen Kudu Maso-Gabashin Turai a Antalya

An fara Babban Taron Hadin Kan Kasashen Kudu Maso-Gabashin Turai a Antalya

A garin Antalya na Turkiyya Shugabannin Kasashen Kungiyar Hadin Kan Kasashen Kudu Maso-Gabashin Turai sun fara gudanar da Babban Taro.

Taron na wannan shekarar da ake yi karkashin Turkiyya da ke Shugabantar Kungiyar, ya fara tare da ganawar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu tare da sauran takwarorinsa.

Cavusoglu ya tarbi Ministocin inda suka gudanar da hoton zumunci, bayan haka kuma suka fara ganawa.

Daga baya kuma Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Recep Tayyip Erdogan zai jagoranci Shugabannin Kasashen Kungiyar don tattaunawa.


News Source:   ()