An bayyana bude wuta kan jirgin saman Itali a lokacin da yake tashi daga filin jiragen saman Kabul Babban Birnin Afganistan.
Bayanan da Rueters suka samu daga jami'an tsaron Italiya sun bayyana cewa, babu wani abu da ya samu jirgin sakamakon harin.
Wani dan jaridar Italiya da ya zanta da tashar Sky 24 an bude wutar ne 'yan mintuna bayan da jirgin ya tashi dauke da fararen hula 100 'yan kasar Afganistan.
Mahukuntan Afganistan sun ce, an yi harbin ne don tarwatsa cincirindon mutanen da ke filin jiragen saman Kabul, ba wai jirgin aka nufa ba.
Tun bayan da Taliban ta kwace iko da kabul mutane suke ta tururuwar guduwa daga kasar.