Ministan Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya bayyana cewa, nan da karshen watan Fabrairu kasar za ta biya bashin dala miliyan 200 da Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ke bin ta.
Blinken ya yi jawabi a wajen taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da aka ka gudanar kan samar da daidato wajen rarraba alluran riga-kafin Corona inda ya ce za su yi aiki da dukkan kawayensu wajen yaki da annobar Corona.
Blinken ya bayyana irin muhmmancin da WHO ke da shi wajen assasa tushen kiwon lafiya mai nagarta a duniya, kuma Amurka za ta bayar da tata gudunmowar ga shirin yaki da Corona na Duniya.