Amurka na shirin janyewa Iran takunkuman tattalin arziki

Amurka na shirin janyewa Iran takunkuman tattalin arziki

Amurka na shirin janye takunkumin tattalin arziki da ta kakabawa Iran sakamakon kokarin sake kulla yarjejeniyar Nukiliya

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Ned Price ya zanta da manema labarai inda ya yi duba zuwa ga tattaunawar da ake yi kan shirin Nukiliyar Iran a Vienna Babban Birnin Ostiriya.

Price ya ce, Amurka ba ta gaggawa don tattaunawa da Iran, kuma a shirye ta ke da ta fuskanci dukkan wahalhalun da ke tattare da tattaunawar, kuma suna fatan za a kare bukatun Amurka a yayin tattaunawar ta Vienna.

Price ya kara da cewa, suna shirin janyewa Iran wasu takunkumai, suna daukar matakan dawo da Iran ga yarjejeniyar Nukiliya da aka kulla da iya.

Kakakin ya ci gaba da cewa, ya zuwa yanzu ba zai bayyana wani bangare na takunkumin da za a janye ba, kuma ba za su mika bukatu su kadai idan har Iran ba ta cika sharuddan dawowa ga yarjejeniyar ba.


News Source:   ()