Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 52 a Nijar

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 52 a Nijar

Mutane 52 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar da mamakon ruwan sama ya janyo a Nijar.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta bayyana cewa, ambaliyar ruwa da mamakon ruwan saman da aka yi a tsakanin watan Yuni da 11 ga Agusta ta illata mutane dubu 50,305 a kasar.

Sanarwar ta ce, gidaje dubu 5,694 ne suka lalace, mutane 52 suka mutu yayinda wasu 34 suka samu raunuka.

Yamai Babban Birnin Nijar ne ambaliyar ta fi shafa, an kuma bayyana a daren da ya hada Talata da Larabar makon nan ruwa mai yawan kilogram 70 zuwa 140 ya zuba a waje mai girman mita 1.

Ana yawan samun ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama da ake yi a Nijar a tsakanin watannin Yuni da Satumba.

A shekarar da ta gabata ambaliyar ruwan ta illata mutane dubu 350 inda mutane 73 kuma suka mutu.


News Source:   ()