Mutane 302 sun rasa rayukansu ambaliyar ruwan da ta afku a jihar Hinan da ke China.
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya rawaito wani jami'in gwamnatin China na cewa, sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku mutane 292 sun sake mutuwa a garin Jingjou wanda hakan ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 302.
Sanarwar ta kara da cewa, ana ci gaba da neman wasu mutanen 50 da suka bata.
Tun daga 17 ga Yuli ake samun mamakon ruwan sama a jihar Hinan da ke China inda a ranar 20 ga Yuli ambaliyar ruwa ta barke.
Ruwa ya mamaye hanyar jiragen kasa ta garin Jingjou inda mutane 14 suka mutu.