Sakamakon mamakon ruwan sama, gidaje da dama, gine-ginen gwamnati da wuraren sana'a sun rushe tare da lalacewa a jihar Gadarif da ke gabashin Sudan.
Kamfanin dillancin labarai na Sudan ya rawaito mahukuntan garin Fav na cewa, sakamakon mamakon ruwan saman da aka samu wanda ya janyo ambaliyar ruwa, gidaje dubu 1,500a makarantu 20 sun rushe, kuma shanu dubu 1,300 sun mutu.
Daruruwan kadada na gonaki sun kasance a karkashin ruwa inda aka samu katsewar lantarki a garin.
Ma'aikatar Albarkatu Ruwa da Ban Ruwa ta SUdan ta sanar da cewa, kogin Nil ya cika makil, a saboda haka ta gargadi jama'a da su kula sosai.
A tsakanin watannin Yuni da Oktoban kowacce shekara ana samun mamakon ruwan sama a Sudan wanda ya kan janyo ambaliyar.
A shekarar da ta gabata mutane 138 ne suka inda sama da gidaje dubu 100 suka samumatsala sakamakon ambaliyar da ta afku a kasar.