Adadin wadanda da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Turkiyya ya karu zuwa mutane 70.
Sanarwar da aka fitar daga Hukumar Yaki da Ibtila'o'i da Bayar da Agajin Gaggawa (AFAD) ta ce, mutane 60 ne suka mutu a Kastamonu, 9 a SÄ°nop da 1 a Bartin.
Sanarwar ta ce, ana ci gaba da yiwa mutane 8 magani a asibiti.
Haka zalika ana ci gaba da aiyukan nema da kubutar da jama'a a lardunan 3 da ke Yankin Tekun Majliya.
News Source: ()