A Afirka, mutane biliyan 1,2 ne ke cikin hatsari sakamakon rashin kyakkyawan yanayin kula da lafiya.
Shugaban Bankin Cigaban Afirka Akinwumi Adesina ya sanar da cewa, 'yan kasashen Afirka biliyan 1,2 na fuskantar hatsari sakamakon yadda babu kayan yaki da magance cutar Corona a nahiyar.
Adesina ya kara da cewa, suna gwagwarmaya da matsalolin kula da lafiya da na tattalin arziki, kuma za su karfafa taimakon da suke baiwa kasashen Afirka.
Adesina ya kuma ce, AfDB zai bayar da gudunmowa da taimako wajen samar da alluran riga-kafin Corona a Afirka da kuma harkar kiwon lafiya a nahiyar, kuma kaso 51 na gine-ginen gwamnati a nahiyar ne suke da ruwa mai tsafta da hasken lantarki.
Haka zalika Adesina ya ce, kuma Afirka na shigar da kaso 60 zuwa 70 na magungunan da ake amfani da su.