Adamu: Rashin tsaftataccen ruwan sha na barazana ga miliyoyin 'yan Najeriya

Adamu: Rashin tsaftataccen ruwan sha na barazana ga miliyoyin 'yan Najeriya

Sama da mutane miliyan 60 ne su ke fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka a Najeriya sakamakon rashin samun tsaftataccen ruwan sha.

Ma'aikatar Albarkatun Ruwa ta Najeriya ta fitar da alkaluma da ke tabbatar da har yanzu miliyoyin 'yan kasar ba sa samun ruwan sha mai tsafta.

Ministan Albarkatun Ruwa Sulaiman Hussaini Adamu ya sanar da cewa, a kowacce shekara daruruwan yara 'yan kasa da shekaru 5 na mutuwa a Najeriya sakamakon rashin samun ruwan sha mai tsafta.

Adamu ya shaida cewa, wannan yanayi ne mai ban tsoro, kuma za su ci gaba da aiyukan samarwa da jama'a tsaftataccen ruwan sha.


News Source:   ()