Mutane dubu 1,941 ne suka rasa rayukansu, wasu sama da dubu 7 kuma sun jikkata sakamakon girgizar kasa mai karfin awo 7,2 da ta afku a Haiti a ranar Asabar din da ta gabata.
Mahukunta sun bayyana cewa, an samu rushewar gidaje da dama a kasar sakamakon girgizar kasar.
Hukumar Kare Fararen Hula ta Haiti ta shaida cewa, adadin wadanda girgizar kasar ta yi ajali ya kai dubu 1,941, wadanda suka jikkata kuma sun kai dubu 6,900.
Gwamnatin kasar ta yi kira ga kasashen duniya da su taimaka musu.
Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Amurka (USGS) ta bayyana cewa, girgizar ta afku a yankin mai nisan kilomita 12 daga sansanin Saint-Jean-du-Sud.
An jiyo alamun girgizar kasar a Port-au-Prince Babban Birnin Haiti inda jama'a suka fita kan tituna a firgice.
Girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 10, kuma Hukumar USGS ta janye gargadin yiwuwar afkuwar tsunami da ta yi tun da farko.
An aike da jami'an ceto zuwa yankin, kuma Firaministan Haiti Ariel Henry ya sanar da dokar ta baci ta wata 1 a fadin kasar.
Haka zalika an aika da jami'ai daga Amurka, sannan an tura kayan magunguna tan 15,5 daga Mekziko zuwa kasar.