Ya zuwa mutane 37 ne suka mutu sakamakon ambalir ruwan da ta afku a makon da ya gabata a Beljiyom.
Hukumar Magance Ibtila'o'i ta Kasa ta bayyana cewa, a yanzu mutane sun sake mutuwa wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 37 sakamakon ambaliyar ruwan.
A baya mahukunta sun bayyana ba a ga mutane 473 musamman a gabashin kasar amma a yanzu an ce mutane 6 kawai ake ci gaba da nema.
Ana ci gaba da neman mutanen 6 inda 'yan sanda da masu kunna nutso suke ta kokarin gano su.
A makon da ya gabata ne aka samu mamakon ruwan sama a Beljiyom inda ambaliyar ruwa ta afku a garuruwan Liege, Vervier, Spa da Namur.
News Source: ()