Ziyarar ministar harkokin wajen Jamus a yamamcin Afirka

Ziyarar ministar harkokin wajen Jamus a yamamcin Afirka
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock tana fara ziyarar aiki a kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar da ke yankin yammacin Afirka.

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock tana fara ziyarar aiki a kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar da ke yankin yammacin Afirka. A birnin Bamakon na Mali Baerbock za ta gana da Assimi Goïta shugaban gwamnatin mulkin soja ta wucin gadi da ministan harkokin wajen kasar Abdoulaye Diop. Sannan ta gana da wakilan Tarayyar Turai kan sojojin Jamus kimanin 300 da ke ba da horo a kasar ta Mali mai fama da tashe-tahsen hankula.

A birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock za ta gana da Shugaba Mohamed Bazoum da ministan harkokin wajen kasar Hassoumi Massoudou inda za a tattauna kan batun dakarun Jamus da ke yankin sannan za ta gana da wakilan kungiyoyion fararen hula a duk kasashen biyu. Yankin dai na fama da karin karancin abinci bayan kutsen da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine.

 


News Source:   DW (dw.com)