Zelenskyy ya godewa EU na sawa Rasha takunkumi

Zelenskyy ya godewa EU na sawa Rasha takunkumi
Shugaban kasar Ukraine ya yi kira da a duba yuwar tsari na bakwai na takunkumin EU a kan kasar Rasha abyan cimma matsaya kan tsari na shida, yana mai bayyana Rasha a matsayin ‘yar ta’adda.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya godewa kungiyar Tarayyar Turai EU kan shirinta na shida da ya cimma mastayar kara wa kasar Rasha takunkumin hana sayan man feturta.

Duk da cewa Amirka ta yi barazanar turawa Ukraine samfurin makaman roka na zamani, amma Shugaba Zelenskyy ya bukaci kasashen yamma su kara wa Rasha takunkumi na bakwai, inda ya kwatanta Rasha da 'yar ta'adda.

Yanzu haka dai asusun kula da kananan yara na MDD Unicef ya ce fiye da yara miliyna biyar a Ukraine na cikin wani hali saboda tsananin yaki.


News Source:   DW (dw.com)