Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine, ya ce matakin diflomasiyya ne kadai zai iya warware matsalar da ke tsakanin kasarsa da Rasha ba kuma karfin soja kadai ba.
A jawabin da ya gabatar a ranar Asabar, Shugaba Zelenskyy ya kuma nuna bukatar shigar da Ukraine cikin kungiyar Tarayyar Turai.
Jawabin nasa ya zo ne yayin da Amirka ta amince da bai wa kasar dala biliyan 40 a matsayin tallafi saboda yakin da take fama da shi.
Kawayen Ukraine na yammacin duniya dai na ci gaba da bai wa kasar tallafin makaman yaki ne tare da kakaba manyan takunkuman karya tattalin arziki kan Rasha.
Shugaba Zelenskyy ya ce wasu batutuwan na bukatar zama kan teburi ne, ba kuma tsananin amfani da karfin wuta daga tsinin bindiga ba.
A halin da ake ciki dai Rasha ta ce ta yi nasarar lalata wani tarin makamai, wadanda kasashen Turai da Amurka suka aika wa Ukraine a yankin arewa maso yammacin kasar.