Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya gode wa Kungiyar Tarayyar Turai EU kan shirinta na shida da ya cimma mastayar kara wa kasar Rasha takunkumin hana sayan man feturta.
Duk da cewa Amirka ta yi barazanar tura wa Ukraine samfurin makaman roka na zamani, amma Shugaba Zelensky ya bukaci kasashen yamma su kara wa Rasha takunkumi na bakwai, inda ya kwatanta Rasha da 'yar ta'adda.
Yanzu haka dai, Asusun Kula da Kananan Yara na MDD Unicef ya ce fiye da yara miliyan biyar a Ukraine na cikin wani hali saboda tsananin yaki.