Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya ba da tabbacin cewa Washington na neman samar da zaman lafiya mai dorewa a Ukraine a yayin ganarwar da ya yi a karon farko da Volodymyr Zelensky a jiya Juma'a.
Wannan ganawa tsakanin shugaban Ukraine da wakilin Donald Trump na zuwa ne a daidai lokacin da fadar mulki ta Kiev ta girgiza biyo bayan tattaunawa ta waya da Shugaba Putin ya yi da takwaransa na Amurka a wannan mako.
Zelensky da JD Vance sun ce sun gamsu da tattaunawar da suka yi a daura da taro kan manufofin tsaro da ke gudana a birnin Munich na kasar Jamus sannan kuma sun ba da tabbacin cewa za su sake yin wata ganawa a makonni ko kuma watanni masu zuwa.