Zelensky ya bukaci kasashen yamma su cika alkawarinsu

Shugaba Zelensky ya ce a yan kwanankin baya-bayan nan Rasha ta kara kaimi a hare.haren da take kai musu, wanda ya ce sama da rokoki 700 da jirage marasa matuka 600 ne aka harbo su daga yankunan Rasha ya zuwa cikin kasar.

Shugaban na Ukraine ya ce matsayar da aka cimma a taron kungiyar tsaro ta NATO a Washington da kuma na Ramstein na kasar Jamus don  samar musu da makaman kare sararin samaniya har yanzu shiru suke ji. 

Ko a wannan makon Shugaba Volodmyr Zelensky ya ce ya tattauna batun baiwa kasarsa damar sarrafa makamanta na kare sararin samaniya da ma masu linzami.  

Karin Bayani:Rasha ta kai wa Ukraine kazamin hari da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka


News Source:   DW (dw.com)