Shugaban na Ukraine Volodmyr Zelensky ya bukaci mahalarta babban taron tattalin arziki na duniya da aka fara a birnin Davos na kasar Switzerland kan su taimaka masa wajen kawo karshen yakin da Rasha ta kaddamar a kasarsa.
Shugaba Zelensky ya bukaci hakan ne a lokacin da ya yi jawabi ga mahalarta taron ta kafar bidiyo, inda ya ce yana son ganin kasashen sun dakatar da hulda da daukacin bankunan kasar Rasha.
Har wa yau, shugaban na son ganin an yanke duk wata huldar cinikayya da ake Rasha wanda hakan zai zama izina ga duk wata kasa da ke da shirin daukar irin wannan mataki, don ta san cewa ba za a raga mata ba.
A nasa ganin inda tun da farko an yi wa Rasha rubdugu da ba a kai ga halin da ake ciki ba a yanzu haka. Ana ci gaba da zargin Rasha da daukar fansa na dakatar da fitar da abinci daga kasar da ma ta Ukraine. Wanda ake ganin dole ne mahaltar wannan taron su lalubo hanyar warware matsalar.